Talata 26 Mayu 2026 - 23:25
Haɗin Kai Tsakanin Shi'a da Sunna Shamaki ne Mai Karfi ga Makircin Makiya

Hauza/ Ayatullah Sayyid Kazim Nourmofidi, Wakilin Waliyyul Faƙih a lardin Golestan kuma Limamin Juma'ar Gorgan, ya bayyana cewa hadin kai tsakanin mabiya mazhabar Shi’a da Sunna wani katanga ne mai karfi da ke dakile makircin makiya.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran  Hauza daga Gorgan, an gudanar da taron karramawa da jinjina ga malaman makarantun addini na mabiya Sunna na lardin Golestan a ranar Litinin, 4 ga watan Khordad, 1405 (24 ga Mayu 2026). Taron ya gudana ne a gidan Baituz-Zahra (S.A) dake Gorgan, tare da halartar Ayatullah Sayyid Kazim Nourmofidi.

Wannan taro, wanda aka shirya domin daukaka matsayin ilimi da na ruhaniya na malaman addini, Ayatullah Nourmofidi ya yi nuni da babban nauyin da ya rataya a wuyan malamai a wannan lokaci mai sarkakiya, inda ya jaddada bukatar daukaka matakin ilimi da kuma bayyana koyarwar addini ta hanyar da ta dace da zamani.

Wakilin Waliyyul Faƙih a lardin Golestan, yayin da yake nuna farin cikinsa game da yanayin kauna da fahimtar juna dake tsakanin malaman Shi’a da Sunna, ya bayyana cewa: "Gudanar da irin wadannan taruka ba wai kawai yana faranta wa Ubangiji Madaukaki da Manzon Allah (S.A.W.A) rai ba ne, a'a, hakan wata alama ce ta zahiri ta hadin kai da 'yan uwantaka ta addini, wanda hakan ke zama shamaki mai karfi ga dukkan shirin makiya na rarraba kan musulmi."

Ayatullah Nourmofidi ya ci gaba da bayyana muhimmancin "Isar da sako a bayyane" (Tabligul Mubeen) a duniyar yau, inda ya kara da cewa: "Malaman addini ya kamata su yi amfani da ilimin zamani da sabbin hanyoyin sadarwa domin bayyana koyarwar Musulunci ta yadda za su kasance masu haske, tasiri, da shiriya ga matasa da al'ummar yau."

A karshen taron, an karrama malaman makarantun addini na Ahlus-Sunna sakamakon kokarinsu na yada koyarwar addini da kuma karfafa dankon zumunci a lardin Golestan.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha